Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tsarin zuba jarin waje mai inganci da aka kayyade zai kara kuzarin kasuwar Sin
2019-11-22 19:30:03        cri

A yau Juma'a ne gidan rediyon kasar Sin, ya gabatar da wani sharhi mai taken "Idan tsarin jadawalin sassan zuba jarin waje da aka kayyade ya kyautata, hakan zai kara kuzari ga kasuwar kasar Sin", inda a cikin sa aka yi nuni da cewa, yau 22 ga wata, gwamnatin kasar Sin ta fitar da jadawalin sassan zuba jarin waje da aka kayyade na shekarar 2019, lamarin da ya alamta cewa, tsarin jadawalin sassan zuba jarin waje da aka kayyade yana samun kyautatuwa. Har ila yau sharhin ya nuna cewa, kasar Sin ta kuduri aniyar kyautata muhallin kasuwanci a kasar.

A cikin sabon jadawalin, an kara mai da hankali kan bude kofa ga waje a bangaren samar da hidima, ko shakka babu hakan zai ingiza ci gaban tattalin arziki mai inganci a kasar ta Sin, haka kuma zai kara kuzari ga kasuwar kasar, ta yadda za ta kara jawo hankalin 'yan kasuwa a fadin duniya.

Sharhin ya jaddada cewa, bisa kyautatuwar tsarin, kamfanonin jarin waje za su samu karin damammaki a kasuwar kasar Sin, kuma ita ma kasar Sin tana kara kokari, domin tsara salon tattalin arzikinta wanda zai dace da ma'aunin kasa da kasa mai inganci, kana kasar Sin tana kara zurfafa kwaskwarima, da bude kofa ga waje, domin ciyar da tattalin arzikin kasa da ma tattalin arzikin duniya gaba yadda ya kamata.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China