Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kira babban taron fasahar 5G na kasa da kasa na shekarar 2019 a birnin Beijing
2019-11-22 13:37:01        cri


Yanzu ana gaggauta yunkurin yin kwaskwarima a fannin kimiyya da fasaha da sana'ar sadarwa a sabon zagaye. A matsayinta na sabuwar fasahar sadarwar tafi-da-gidanka, fasahar 5G za ta canja yanayin samar da kayayyaki da zaman rayuwar bil Adam, kana da inganta rayuwar bil Adama bisa tsarin zamani na hadewa da juna. Bisa kiyasin da hukumomin da batun ya shafa suka yi, a cikin shekaru 5 masu zuwa, fasahar 5G za ta ba da gudummowar sama da dala triliyan 3 ga karuwar GDPn na duk duniya, kana ya zuwa shekarar 2035 kuma, fasahar 5G za ta kai darajar dala triliyan 12, za kuma ta samar da guraban ayyukan yi miliyan 22 ga duniya baki daya.

 

Ministan kula da harkokin kimiyya da fasaha na kasar Sin Wang Zhigang ya bayyana cewa, idan aka waiwayi yadda aka samu ci gaban fasahar 5G, ana iya cewa, hukumomi da kamfanonin da batun ya shafa na kasar Sin sun taka muhimmiyar rawa kan nazari da amfani da fasahar da kuma yin cudanya da hadin kai a tsakanin kasa da kasa a wannan fannin. Wang ya ce,

"Ma'aikatar kula da harkokin kimiyya da fasaha za ta hada kai tare da hukumomin da batun ya shafa da kananan hukumomi don inganta ayyukan nazari da habaka da yin amfani da fasahar 5G, da kuma yin cudanya da hadin kai a tsakanin kasa da kasa a wannan fanni. Wasu kamfanonin sadarwa, ciki har da China Mobile, China Unicom, China Telecom, Huawei and ZTE da dai makamantansu suna sa himma wajen shiga aikin tsara ma'aunin bai daya na kasa da kasa kan fasahar 5G, bisa albarkatun fasahohin da suka samu a fasahar 3G da 4G, da kuma kwarewarsu kan habaka muhimman fasahohi, sun yin kokari tare da wasu abokan hadin kai na kasa da kasa kamar su kamfanonin Ericsson, Nokia, Samsung, don gudanar da aikin bincike, ta yadda suka bayar da muhimmiyar gudummowa kan yin kirkire-kirkire a wasu muhimman ayyuka game da fasahar 5G, hakan ya sa suka samu amincewa sosai daga bangarori daban daban na duniya."

A shekarar 2019, gwamnatin kasar Sin ta bayar da lasisin samar da fasahar 5G ta fannin harkokin kasuwanci ta kuma kaddamar da shi a hukumance. Ya zuwa yanzu, an kafa tashoshin adana bayanan fasahar 5G har dubu 113 a duk fadin kasar, ana ganin cewa, ya zuwa karshen shekarar bana, adadin zai kai zuwa dubu 130, yawan masu amfani da fasahar 5G ya riga ya kai dubu 870. Ministan masana'antu da sadarwa na kasar Sin Miao Wei ya bayyana cewa, bude kofa da hada kai za su ci gaba da kasancewa ra'ayin bai daya na kasa da kasa wajen ciyar da fasahar sadarwar tafi-da-gidanka a nan gaba, kasar Sin na maraba da kamfanoni da hukumomin nazari na duniya su more nasarorin da aka cimma sakamakon ci gaban fasahar 5G. Miao ya ce,

"Kasar Sin ba ta taba takaita kason da kamfanoni za su samu a kasuwanninta ba, kuma ba za ta yi haka ba. Dukkan kamfanoni, ciki har da na kasar Sin da na ketare, za su yi takara cikin adalci bisa ka'idar gabatar da tanda. Ma'aikatar masana'antu da sadarwa na daukar nauyin sa ido kan tanda da kamfanonin sadarwa suka gabatar, bisa ka'idar adalci da yin komai bayyane, kuma ba za ta canja irin wannan ka'ida ba. Duk kamfanonin da suke fatan kara kason da za su samu a kasuwar fasahar 5G, ya dace su mai da hankali kan ingancin kayayyaki da hidimarsu, da takardar neman tanda. Muna nuna sahihanci don maraba da kamfanoni da hukumomin nazari na duniya don su yi kokari tare da mu da nufin raya tsarin fasahar 5G na kasar Sin yadda ya kamata, da kuma more nasarorin da za a cimma sakamakon ci gaban fasahar."

Shugaban tawagar wakilan EU dake nan kasar Sin Nicolas Chapuis shi ma na ganin cewa, hadin kai a fannin fasahar, zai samar da gajiya ga bangarori daban daban, don haka ya kamata kasa da kasa su kara kokari a wannan fannin.

"A gani na, yanzu muna cikin wannan zamani, wato Turai da kasar Sin sun iya samun moriyar juna ta hadin kan fasahar 5G. Ya kamata dukkan kamfanonin sadarwa na duniya su yi kokari a wannan fannin, wannan shi ne sakamakon da gwamnatoci da jama'ar kasashe daban daban ke fatan cimmawa." (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China