Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dabarun Sin na taimakawa ci gaban duniya
2019-11-21 19:43:21        cri

Yau Alhamis gidan rediyon kasar Sin ya gabatar da wani sharhi mai taken "Dabarun kasar Sin suna ci gaba da ingiza ci gaban duniya", inda aka yi nuni da cewa, yayin dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin kirkire-kirkire, wanda aka kaddamar yau a nan birnin Beijing, kasar Sin tana ci gaba da gabatar da dabarunta, domin dakile kalubalen da daukacin kasashen duniya ke fuskantar a bangarori hudu, wato tafiyar da harkokin kasa, da samun aminci, da shimfida zaman lafiya da kuma samun ci gaba.

Kasar Sin tana kokarin neman samun sabbin dabarun ingiza ci gaban duniya, inda ta jaddada cewa, ya dace a kiyaye tsarin kasa da kasa karkashin jagorancin MDD, domin tsara wani shirin tafiyar da harkokin kasa da kasa bisa adalci, kuma kasar Sin tana ganin cewa, ya kamata a mai da hankali kan kirkire-kirkire, da bude kofa ga ketare, da kuma yi wa juna afuwa, domin samun ci gaba tare.

Kaza lika kasar Sin na da ra'ayin cewa, abu mafi muhimmanci shi ne a nuna wa juna sahihanci, da aminci da fahimtar juna, ban da haka, kamata ya yi a yi kokari tare, domin cimma burin wanzar da zaman lafiya a fadin duniya, ta hanyar gudanar da hadin kai.

Dabarun da kasar Sin ta aiwatar, sun samu amincewa daga wajen mahalarta taron, lamarin da ya sake shaida cewa, bude kofa ga waje, da gudanar da hadin kai, da yin kirkire-kirkire, da nuna hakuri ga juna, za su taka babbar rawa ga ci gaban duniya. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China