A yau Alhamis, aka bude taron dandalin tattalin arziki na zamani na kasa da kasa karo na 2 a Beijing. Kimanin mahalarta da suka hada da jami'an gwamnatoci, shugabanni da wakilan kamfanoni, da kwararrun masana 500 daga kasashen duniya da shiyyoyi 50 ake sa ran za su halarci taron. Mataimakin shugaban kasar Sin Wang Qi Shan ya gabatar da jawabin bude taron. Wakilinmu Ahmad Inuwa Fagam ya halarci bikin ga karin bayanin da ya aiko mana.