Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanonin kere-kere da na samar da hidima na Sin sun ninka cikin shekaru 5
2019-11-20 19:12:37        cri

Ofishin yada bayanai na majalissar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da wasu alkaluman kididdiga dake nuna cewa, adadin kamfanonin kere-kere da na samar da hidima na kasar sun ninka cikin shekaru 5.

Karuwar yawan na su a cewar ofishin, ta kai ta kaso 100.7 bisa dari, idan aka kwatanta da wanda aka samu yayin kididdigar alkaluman tattalin arziki na shekarar 2013.

Cikin bayanin da ofishin ya fitar, karkashin kididdigar alkaluman tattalin arziki karo na 4 a Larabar nan, mai kunshe da ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar, an nuna cewa, a karshen shekarar 2018, adadin wadannan kamfanonin ya kai miliyan 21.8, adadin da ya ninka wanda ake da shi a shekarar 2013.

Bayanin ya nuna cewa, sassan da suka fi samun karuwar kamfanonin sun hada da na sayar da kayan sari, da fannin kere kere, da na ba da haya, da na hidimomin kasuwanci.

Ya zuwa karshen shekarar 2018, an samu karuwar kamfanonin kere keren hajoji ta hanyar amfani da fasahohin zamani har 33,573, karuwar da ta kai kaso 24.8 bisa dari, idan an kwatanta da adadin na shekarar 2013. Wadannan kamfanoni dai sun kara yawan jarin su a harkokin bincike da samar da ci gaba, da kaso 75 bisa dari cikin shekarun 5.

Kididdigar sassan ci gaban tattalin arzikin kasar Sin dai na samar da cikakkun bayanai, game da adadin kamfanoni kere-kere da samar da hidima, tana kuma ba da damar yin hasashe game da yanayin tattalin arzikin kasar a nan gaba, musamman ma wajen shirya dabarun bunkasuwa na gaba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China