Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan kasuwan Sin sun shiga cikin jerin manyan kwararru na duniya
2019-11-20 14:07:29        cri
Thinkers50, wata fitacciyar hukumar dake tantance manyan kwararrun 'yan kasuwa na kasa da kasa, ta sanar da jerin sunayen manyan kwararrun masana harkokin cinikayya na shekarar 2019.

Wasu 'yan kasuwan kasar Sin biyu tare da takwarorinsu na wasu kasashe da shiyyoyin duniya 15 sun shiga cikin jerin sabbin manyan kwararrun masana harkokin cinikayya 50 na duniya.

Zhang Ruimin, shugaban hukumar gudanarwar rukunin kamfanonin Haier, ya shiga cikin jerin kwararrun masu kamfanoni na duniya a karo na uku, inda ya zo matsayi na 15 a bana.

Zeng Ming, tsohon babban jami'in rukunin kamfanonin Alibaba, shi ne ya zo na 28 a cikin jerin sunayen a karon farko.

An fara kaddamar da shirin na Thinkers50 ne a shekarar 2001 wanda hukumomin Des Dearlove da Stuart Crainer, dukkansu sun samu amincewa a matakin kasa da kasa a matsayin hukumar kwararru ta Birtaniya. Ana wallafa kididdigar na jerin kwararrun masana harkokin kasuwanci 50 na duniya ne duk bayan shekaru biyu. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China