Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta raba yuan biliyan 113.6 domin yaki da talauci
2019-11-18 19:46:04        cri

Gwamnatin tsakiya ta kasar Sin, ta amince da rarraba wani bangare na kudaden da aka tanada domin yaki da talauci na shekarar 2020 ga kananan hukumomin kasar.

Rahotanni daga ma'aikatar kudin kasar sun bayyana cewa, an rarraba kudin da ya kai Yuan biliyan 113.6, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 16.2, ga yankuna 28 dake matakan larduna, adadin da ya kai kaso 90 bisa dari, na adadin da aka kashe a wannan fanni a shekarar nan ta 2019.

Alkaluman da ma'aikatar kudin ta fitar sun nuna cewa, za a kashe Yuan biliyan 14.4 a fannin tallafawa yankuna dake cikin matsanancin talauci, ciki hadda Tibet, da Xinjiang, da wasu yankunan lardin Sichuan, da Yunnan da Gansu.

Ma'aikatar kudin ta ce, ikon nazari da kuma amincewa a yi amfani da kudaden yaki da fatarar, na hannun gwamnatocin gundumomi, kana ba a yarda a yi amfani da kudaden ta wani fanni sabanin ayyukan rage talauci ba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China