Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wani dan bindiga ya halaka mutane 4 a California
2019-11-18 16:21:46        cri
Rahotanni daga California na kasar Amurka na cewa, a kalla mutane hudu ne suka mutu kana wasu shida kuma suka ji rauni, a wani harbin kai mai uwa da wabi da aka kai kan wani iyalai da suka taru a harabar bayan gidansu jiya Lahadi a Fresno dake jihar California, kilomita 350 arewa da birnin Los Angeles.

Wani jami'i daga hukumar sashen 'yan sandan Fresno mai suna Bill Dolley, ya shaidawa manema labarai cewa, 'yan sanda sun samu rahoton harbin ne, kafin karfe 6 na yamma agogon wurin.

Ya ce, lamarin dai ya faru ne, lokacin da wasu gungun mutane suka taru a harabar bayan gida suna kallon wasan kwallon kafa. Sai wani mutum da ba a san asalinsa ba, ya sulale ya shiga gidan ya kuma hude musu wuta,kafin daga bisani ya arce. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China