Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude taron kolin jagororin kafofin watsa labarai na duniya a Shanghai
2019-11-18 14:03:10        cri
A yau ne, aka bude taron kolin jagororin kafofin watsa labarai na duniya (WMS) a birnin Shanghai dake yankin gabashin kasar Sin.

Cai Mingzhao, shugaban zartaswar WMS kana shugaban kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin, ya jagoranci taron tare da gabatar da jawabi.

Manyan jami'an hukumomin watsa labarai 13 daga kasashe 11, da suka hada da kamfanin dillancin labarai na AFP na kasar Faransa, da kafar watsa labarai ta Al Jazeera, da Associated Press, da BBC da Kyodo News, da Naspers daga Afirka ta kudu, da Rukunin kafar watsa labarai ta Folha de S.Paulo na kasar Brazil, da kamfanin dillancin labarai da rediyo na kasa da kasa na Sputnik, da kamfanin dillancin labarai na kasar Rasha(TASS) da Hindu Group, da ANSA ne suka halarci taron.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China