Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yunkurin Mike Pompeo Zai Kawo Illa Ga Kasarsa
2019-11-17 16:56:53        cri

Ayyukan masu tsattsauran ra'ayi da suka tsananta a yankin Hong Kong na kasar Sin sun riga sun haddasa raunatar da mutane fiye da dari daya, har ma wani farar hula ya mutu. Sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya kyale wadannan ayyuka, har ma ya yi jawabi, inda ya yi amfani da ma'auni biyu kan wannan batu, da kin yin la'akari da tsarin dokoki da jin kai, da tsoma baki kan harkokin cikin gida na kasar Sin a fili, hakan ya shaida yunkurinsa na tada rikici da yin matsin lamba ga kasar Sin ta hanyar batun yankin Hong Kong. Jawabin Pompeo ya shaida cewa, ayyukan masu tsattsauran ra'ayi da aka tsananta a yankin Hong Kong suna da nasaba da masu yaki da kasar Sin na kasar Amurka, mai yiwuwa ne su ne suka tsara wadannan ayyuka.

An jaddada cewa, gwamnatin yankin Hong Kong ta yanke hukunci ga masu aikata laifuffuka domin wannan batu bisa dokoki, hakan ya tabbatar da tsarin dokokin yankin da hakkin dan Adam da 'yancin jama'ar yankin. A yayin ganawa ta 11 a tsakanin shugabannin kasashen kungiyar BRICS, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi nuni da cewa, gwamnatin kasar Sin ta yi imani da tabbatar da ikon mallaka da tsaro da kuma moriyar bunkasuwa, da tsayawa tsayin daka kan manufar Sin daya amma da tsari biyu, kuma bata amincewa sauran kungiyoyin kasashen waje su tsoma baki kan harkokin yankin Hong Kong ba. Bai kamata wasu mutane kamar Pompeo su yi kuskure kan batun ba. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China