Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ra'ayin Sin ya taimaka ga raya tsarin kungiyar BRICS a muhimmin lokaci
2019-11-15 20:10:03        cri
A jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi a gun taron shugabannin kasashen kungiyar BRICS, da ya gudana a Brazilia, fadar mulkin kasar Brazil, ya sake jaddada cewa, ya kamata kasashen kungiyar BRICS su sauke nauyin dake wuyansu a fannonin tattalin arziki, da siyasa, da kuma al'adu, wanda ya nuna kyakkyawar makoma da samar da sabbin shirye-shirye kan zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen kungiyar.

Ya jaddada cewa, ya kamata kasashen kungiyar BRICS su nuna adawa da ra'ayin bada kariya ga cinikayya, da martaba ra'ayin tafiyar da harkokin duniya ta hanyoyin tattaunawa tare kan manyan manufofin hadin kai, kafa dandalin hadin kai tare da kuma more nasarorin da aka cimma kan hadin kai, kana da kara ikon fada a ji da tasiri na sabbin kasashen da tattalin arzikinsu ke bunkasa da kasashe masu tasowa a harkokin kasa da kasa, da kuma maida hankali ga dora muhimmanci kan batun samun bunkasuwa a yayin da ake inganta tsarin tafiyar da harkokin duniya daga manyan fannoni. A cikin shekaru 10 masu zuwa, tilas kasashen kungiyar BRICS za su samu ci gaba mai inganci da kuma amfanawa kansu har ma ga dukkan duniya baki daya. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China