Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zurfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen BRICS da imani da hakikanin mataki
2019-11-14 19:18:32        cri

Yau gidan rediyon kasar Sin CRI ya gabatar da wani sharhi mai taken "Kara zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen mambobin kungiyar BRICS ta hanyar yin amfani da imani da daukar hakikanan matakai", inda aka bayyana cewa, a ranar 13 ga wata yayin bikin rufe dandalin tattaunawa kan masana'antu da kasuwanci na kasashen mambobin BRICS, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi nuni da cewa, huldar abota ta sabon juyin juya halin masana'antu tsakanin kasashen BRICS za ta ingiza hadin gwiwar dake tsakaninsu a nan gaba.

Rahoton ya nuna cewa, huldar abota ta sabon juyin juya halin masana'antu tsakanin kasashen BRICS, za ta kasance daya daga cikin muhimman ayyukan da kasashen suke gudanarwa, tare da sauran ayyuka uku wato raya tattalin arziki, da kiyaye tsaron siyasa da hadin kan al'adu, wannan shawarar za ta biya bukatun sabon juyin juya halin kimiyya da fasaha, da sabbin sana'o'i, haka kuma za ta taimakawa kasashen BRICS su kafa sabon fannin hadin gwiwa a tsakaninsu, tare kuma da samun ci gaban masana'antu tare.

Sharhin ya kara da cewa, kasar Sin ba ta sauya niyyarta ta kara bude kofa ga waje ba, tattalin arizkin kasar shi ma yana ci gaba da samun bunkasuwa cikin lumana, kasar Sin tana cike da imani da kara kokari domin kara zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen BRICS ta hanyar daukar hakikanan matakai, ta yadda za su cimma burin samun ci gaba tare.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China