Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta harba tauraron dan adam 5 zuwa duniyar orbit ta hanyar amfani da roka guda
2019-11-14 14:08:04        cri
A jiya Laraba cibiyar harba tauraron dan adam ta Taiyuan na lardin Shanxi dake arewacin kasar Sin ta harba sabbin taurarin dam adam 5 da ake iya sarrafa su da na'ura daga nesa zuwa duniyar orbit.

An harba taurarin dan adam din guda 5 samfurin Ningxia-1 ta hanyar amfani da na'urar dake daukar roka samfurin Long March-6 guda daya da misalin karfe 3 sauran minti 25 na yamma agogon Beijing.

Taurarin dan adam din na daga cikin ayyukan tauraron dan adam na kasuwanci wanda kamfanin fasahar sadarwa na zamani na Ningxia Jingui ya zuba jarinsa, sannan galibin aikin sabbin taurarin din za su fi shafar fasahar gano wurare ne.

Taurarin dan adam din da na'urar daukar roka din kamfanin DFH ne ya kera su da hadin gwiwar kwalejin fasahar nazarin sararin samaniya ta Shanghai.

Harba taurarin dan adam din da aka gudanar a ranar Laraba shi ne aikin Long March karo na 318 da na'urar dake daukar rokar ta gudanar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China