Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasar Sin ya ziyarci Masar don kyautata dangantaka
2019-11-14 09:53:18        cri

Kasar Sin da Masar sun amince za su zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu da kuma kara karfafa huldar kasashen biyu a yayin da babban jami'in kwamitin majalisar bada shawara kan harkokin siyasar kasar Sin Wang Yang, ya ziyarci kasar ta arewacin Afrika daga ranar 10 zuwa 13 ga watan Nuwamba.

A ganawarsa da shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi, Wang, shugaban kwamitin majalisar bada shawara kan harkokin siyasar kasar Sin (CPPCC), ya yaba da irin ci gaban da aka samu game da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Ya ce kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da Masar wajen daga matsayin cudanyar dake tsakanin kasashen biyu zuwa matsayin koli, da zurfafa mu'amala bisa amincewar juna, da kuma aiwatar da hadin gwiwar dake tsakaninsu karkashin shawarar "ziri daya da hanya daya (BRI)", da yin hadin gwiwa game da batutuwan dake shafar kasa da kasa da shiyya, da karfafa hadin gwiwar wajen yaki da ta'addanci, da ingiza matsayin danganatakar Sin da Masar zuwa cikakkiyar dangantaka bisa matsayin koli.

A nasa bangaren, Al-Sisi, ya yaba da gagarumin ci gaban da aka samu game da matsayin dangantakar dake tsakanin Sin da Masar, ya ce kasar Masar tana goyon bayan shawarar "ziri daya da hanya daya", kuma tana maraba da kamfanonin kasar Sin da su kara zuba jarinsu a Masar. Bugu da kari, ya ce Masar a shirye take ta kara yin hadin gwiwa da kuma koyon matakan yaki da tsattsauran ra'ayi daga kasar Sin. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China