Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutanen da suka rasa matsugunansu a DRC na fama da matsalar keta hakkokinsu
2019-11-13 11:02:13        cri

MDD ta yi gargadin cewa, dubban mutanen da suka rasa matsugunansu bisa tilas a gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo DRC, na rayuwa cikin rashin kariya, inda suke fuskantar matsalar keta hakkokinsu, baya ga rayuwa cikin mawuyacin hali.

Kakakin hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD, Babar Baloch, ya bayyana yayin wani taron manema labarai cewa, mutane 300,000, galibi mata da yara, sun rasa matsugunansu biyo bayan jerin hare-hare da kungiyoyi masu dauke da makamai daban daban suka kai lardunan Ituri da arewacin Kivu a watan Yunin bana.

Ya ce kafin lokacin, an yi kiyasin mutane miliyan 4, adadin da ya dauki kaso 10 na 'yan gudun hijira a duniya, sun bar matsugunansu a fadin Jamhuriyar demokradiyyar Congo.

A cewar kakakin, watanni 5 bayan hare-haren cikin watan Yuni, ana tsaka da fama da kashe-kashe da cin zarafi ta hanyar lalata da sace-sacen mutane da ci gaba da fadace fadace.

Ya ce a watan Oktoba kadai, ma'aikatan hukumar sun samu rahoton keta hakkokin bil adama akalla 1,000 a lardunan 2 dake gabashin kasar. Yana mai cewa, fareren hula na rayuwa cikin fargaba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China