Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban CPPCC ya yi kira ga kamfanonin kasar su zurfafa dangantakar Masar da Sin
2019-11-13 10:31:07        cri

Shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin CPPCC, Wang Yang, ya karfafawa kamfanonin kasar Sin dake Masar gwiwar kara taka rawa wajen zurfafa abota da hadin gwiwa tsakanin kasashen 2.

Wang Yang, ya bayyana haka ne jiya, yayin da yake ganawa da wakilan kamfanonin kasar Sin 25 dake Masar, wadda ya gudana a wani bangare na ziyarar aiki da ya kai Masar.

Jami'in ya kuma yabawa kamfanoni bisa zama babbar gada ta hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Masar.

Wakilan da suka fito daga kamfanonin da suka hada da bankin raya kasar Sin da kamfanin Tianjin Economic-Technological Development da kamfanin fasaha na Huawei da kamfanin gine-gine na China State Construction Engineering da kamfanin hakar ma'adinai na China Petrochemical, sun yi masa bayani kan ayyukansu a Masar tare da ba da shawarwari kan manufofin inganta dangantakar Sin da Masar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China