Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An fara gina wata ma'aikatar sarrafa tarago a jihar Ogun ta Najeriya
2019-11-11 15:17:00        cri
A ranar Asabar da ta gabata ne aka gudanar da bikin kaddamar da aikin gina masana'antar samar da taragon jigilar kaya ta farko a Najeriya, a jihar Ogun dake kudancin kasar.

Kamfanin CCECC na kasar Sin ne ya dauki nauyin gina layin dogon da ya hada biranen Abuja da Kaduna na Najeriya, haka zalika kamfanin na kokarin shimfida wani layi tsakanin biranen Lagos da Ibadan, wanda ake sa ran kammala gina shi a shekara mai zuwa. Sa'an nan don taimakawa Najeriya ta raya harkar samar da taragon jirgin kasa, kamfanin ya dau niyyar zuba jari domin gina wata masana'antar samar da taragun jigilar kaya, a karamar hukumar Kajola ta Jihar Ogun, wadda kuma ake shirin fara aikin da masana'antar tun daga watan Nuwamban shekarar 2020.

A wajen bikin kaddamar da aikin gina masana'antar, wanda ya gudana a ranar Asabar da ta gabata, a Kajola, mataimakin shugaban kasar Najeriya, Yemi Osinbajo, ya yi jawabin cewa,

"Wannan masana'antar da kamfanin CCECC ya zuba jari don ginawa, wata cibiya ce ta samar da tarago, da sauran kayayyakin da ake bukata wajen tafiyar da harkoki masu alaka da jirgin kasa. Ana bukatar wadannan abubuwa don cimma burin gwamnatin tarayyar Najeriya, karkashin jagorancin shugaba Buhari, na zamanintar da layukan dogo a kasar. Muna yabawa gwamnatin kasar Sin, da muhimmin matakin zuba jari da kamfanin CCECC ya dauka. Yadda kuke kokarin daukar matakai, da hangen nesa da kuka nuna, za su sa ku samu riba sosai, tare da haifar da dimbin damammaki ga jama'ar Najeriya."

Masana'antar samar da tarago da ake kokarin ginawa a Kajola za ta sanya wasu fasahohi na kasar Sin, irinsu na samar da kayayyaki masu alaka da layin dogo, da sarrafa tarago, su shiga kasar Najeriya. Haka kuma, za ta taimakawa kasar Najeriya horar da wasu kwararru a fannin sarrafa taragun jirgin kasa. A cewar Jiang Yigao, babban manajan reshen Najeriya na kamfanin CCECC, za a gudanar da ayyuka irinsu walda, da hada kayayyaki, da fesa fenti, da gwajin amfani da tarago a cikin masana'antar. Ya ce,

"Kamfanin CCECC ya dauki nauyin wasu ayyuka na zamanintar da layin dogon Najeriya, da na gina layukan Abuja-Kaduna da Lagos-Ibadan. Wadannan layuka suna taimakawa raya tattalin arzikin Najeriya, da bunkasa masana'antu masu alaka da layin dogo. Sa'an nan wannan masana'antar samar da taragon da za a kafa, wani bangare na shirin zamanintar da layukan dogon Najeriya, kuma wani gwaji ne da muke yi a Najeriya, don samar da karin guraben ayyukan yi, da kuma kara zamanintar da harkar layin dogon kasar."

An ce, bayan da aka kammala gina ma'aikatar, za ta iya samar da taragu 500 a kowace shekara, wadanda suka hada da budaddun taragu, da na jigilar kwantaina, da masu daukar kaya masu ruwa-ruwa, da dai sauransu. A cewar ma'aikatar sufuri ta kasar Najeriya, ma'aikatar za ta samar da tarago 220 ga layukan Abuja-Kaduna da Lagos-Ibadan. Dangane da batun, Rotimi Amaechi, ministan sufuri na kasar Najeriya, ya ce,

"Wadannan taragun za su zama irinsu na farko da ake da su a Najeriya. Nan gaba za a kara samar da wasu sabbin nau'ikan taragun. Ta wannan masana'anta, za a samar da guraben aikin yi kimanin 5000. Kuma taragun da za su fito daga masana'antar za su biya bukatun Najeriya, da ma sauran kasashen dake nahiyar Afirka."

Sauran manyan kusoshin da suka halarci bikin kaddamar da aikin gina ma'aikatar sun hada da karamin jakadan kasar Sin dake Lagos, da gwamnonin jihohin dake dab da layin dogo da ya hada Lagos da Ibadan, da dai sauransu. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China