Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Ba za a yarda da yadda aka nuna karfin tuwo ya yi tasiri kan zaben 'yan majalisar dokokin yankuna daban daban na Hongkong ba
2019-11-09 20:37:22        cri

A yau Asabar, Kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin ya watsa wani sharhi mai taken "Ba za a yarda da yadda aka nuna karfin tuwo ya yi tasiri kan zaben 'yan majalisar dokokin yankuna daban daban na Hongkong ba".

Cikin sharhin, an ce yadda wasu masu tada kayar baya ke neman kashe mista He Junyao, wani dan majalisar dokoki a matakin yanki, ya zama barazana ga adalci da tsaro a yankin Hongkong. Duk wata al'umma dake da wayewar kai ba za ta yarda da irin wannan babban laifi ba. Har ila yau, batun nan ya nuna cewa aikin da ya fi muhimmanci da ya kamata a kula da shi nan take a yankin Hongkong, shi ne kokarin kwantar da tarzoma, da maido da tsari da oda a yankin. Ta wannan hanya kadai, za a samu tabbatar da wani yanayi mai adalci da tsaro domin a gudanar da zabe. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China