Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An watsa fim din "babban faretin soja na shekarar 2019" a Girka
2019-11-09 16:47:30        cri
A jiya Jumma'a ne, aka watsa fim mai taken "babban faretin soja na shekarar 2019" a jami'ar Athens ta kasar Girka, wanda ya nuna bikin murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar al'ummar kasar Sin da harshen Girka. Lamarin da ya nuna cewa, an fara watsa wannan fim a kasashen duniya.

Babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG ne ya shirya fim din, wato "babban faretin soja na shekarar 2019". Cikin wannan fim, an nuna muhimmiyar rawar da kasar Sin ta taka cikin shekaru 70 da suka gataba, da kuma yadda al'ummomin kasar suke hada kansu. A halin yanzu, an fassara wannan fim zuwa harsunan kasashen waje sama da 40, ciki har da harshen Girka, domin fara watsa shi a kasashen duniya.

Cikin lokaci mai tsawo da ya gabata, mataimakin shehun malami na kwalejin harkokin soja na jami'ar Athens, Konstantinos Grivas, ya yi nazari kan hanyar neman ci gaba cikin zaman lafiya ta kasar Sin. Inda ya bayyana cewa, cikin 'yan shekarun nan, kasar Sin ta fara zama kan gaba a fannoni da dama a fadin duniya, lamarin da ya sa, kasar ta kasance babbar kasa mai tasiri kan kasashen duniya. Ya ce karfin sojin kasar Sin zai ba da gudummawa wajen kare zaman lafiyar kasa da kasa. Haka kuma, ya ce, idan aka yi nazari kan shawarar "ziri daya da hanya daya" da kasar Sin ta fidda, za a iya gane cewa, Sin tana son hada kan kasa da kasa, a maimakon nuna adawa da sauran kasashen duniya. Yana mai cewa, aikin na da muhimmiyar ma'ana wajen kare zaman karko da inganta ci gaban kasa da kasa. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China