Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kammala taron duniya kan yaki da shan kayan kara kuzari a tsakanin 'yan wasa
2019-11-08 11:20:38        cri

An kammala taro karo na 5 kan yaki da shan kayan kara kuzari a harkar wasanni a jiya Alhamis, inda aka zabi Witold Banka a matsayin sabon shugaban hukumar yaki da shan kayan kara kuzari WADA tare da amincewa da sabuwar dokar hukumar.

Yayin taron, an yi bita tare da amincewa da sabuwar doka da wasu ma'aunai na kasa da kasa na yaki da shan kayan kara kuzari guda 7. Daga cikin Ma'aunan akwai na wayar da kai da sa ido kan sakamako, wadanda wannan ne karon farko da hukumar ta gabatar da su.

Hukumar WADA, ta kaddamar da tsarin bitar dokar da ma'aunan ne a watan Disamban 2017. Sabuwar dokar da ta kunshi gyaran fuska kan hakkokin 'yan wasa da dakunan gwaje-gwajen kayan kara kuzari da hukunci da takunkumi, za ta fara aiki ne a ranar 1 ga watan Junairun 2021.

An kuma wallafa yarjejeniyar Katowice a ranar karshe ta taron, inda ta yi kira ga dukkan masu ruwa da staki a fannin yaki da shan kayan kara kuzari, da suka hada da kungiyoyin wasanni da gwamnatoci da hukumomin yaki da shan kayan kara kuzari da 'yan wasa, su matse kaimi wajen karfafa hadin gwiwa domin kiyaye tsaftar bangaren wasanni. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China