Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rahoto: Yadda Afirka ta ke fadada kasuwanninta na cikin gida ya samar da damammakin zamanantar da tsarin samar da kayayyaki
2019-11-08 10:07:54        cri
Wani rahoto da kungiyar tarayyar Afirka (AU) ta fitar ya nuna cewa, yadda nahiyar Afirka ta fadada kasuwanninta na cikin gida, ya kara samar da damammaki a kokarin da ake na inganta tsare-tsaren samar da kayayyaki a sassan nahiyar.

Da yake jawabi yayin kaddamar da rahoton, kwamishinan kula da harkokin tattalin arziki a kungiyar AU, Victor Harison, ya bayyana cewa, hanzarta raya bangaren samar da kayayyakin nahiyar, yana da muhimmacin wajen cimma manufofin ajandar AU na shekarar 2063.

A ranar Laraba ne dai, hukumar gudanarwar AU tare da hadin gwiwar cibiyar raya kasa ta OECD suka wallafa rahoton farko game da tattalin arzikin Afirka(AfDD) na shekarar 2019, bisa taken, "Cimma burin farfado da al'amura a Afirka". Haka kuma rahoton ya jaddada bukatar hanzarta farfado da tattalin arzikin nahiyar, ta hanyar yin hadin gwiwa mai karfi tsakanin gwamnati da sassa masu zaman kansu.

Rahoton ya kuma bayyana cewa, bukatar abincin da ake sarrafa a shiyyar na karuwa cikin sauri fiye da sau 1.5 kan matsakaicin na duniya. Hakan ya baiwa kamfanoni da dama dake nahiyar da ma wasu sabbi, damar amfani da wadannan damammaki wajen bunkasa.

Haka kuma rahoton na AfDD na wannan shekara, ya bullo da wata dama ta inganta yadda ake samar da kayayyaki ta hanyar mayar da hankali kan raya wuraren da kamfanonin suke gudanar da harkokinsu, da kara samar da cibiyoyin samar da kayayyaki na shiyya, da kara karfin kamfanonin nahiyar, ta yadda za su iya shiga sabbin kasuwanni.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China