Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Peng Liyuan da mai dakin shugaban Faransa sun kai ziyara makarantar sakandaren jamai'ar koyon harsunan waje ta Shanghai
2019-11-06 11:23:40        cri

Jiya Talata, uwar gidan shugaban kasar Sin Peng Liyuan ta gayyaci mai dakin shugaban Faransa Brigitte Macron zuwa makarantar sakandaren jamai'ar koyon harsunan waje ta Shanghai.

Da farko, sun saurari bayanin da shugaban makarantar ya yi kan yadda makarantar ta ke gudanar da ayyukanta da musanyar ra'ayi da makarantun ketare. Daga bisani Peng Liyuan da Brigitte Macron sun amsa tambayoyin da dalibai suka yi musu. Ban da wannan kuma, sun ganewa idonsu yadda daliban suke koyon fasahohin al'adun gargajiya na tarihi da aka gada daga kaka da kakanni.

Peng ta ce, al'adu wata gada ce dake hada tarihi da zamani da ma zukatun jama'a, tana fatan matasan kasashen biyu za su hada al'adun kasashen biyu waje guda don yayata zumuncin kasashen biyu. Brigitte Macron a nata bangare ta ce, fasahohin daliban da kaunar da suke nunawa Faransa sun burge ta sosai, kamata ya yi a karawa matasan kasashen biyu kwarin gwiwa don kara tuntubar juna da yin musanyar ra'ayi. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China