Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ba za ta sauya matsayarta kan yarjejeniyar Paris ba duk da ficewar da Amurka ta yi
2019-11-06 10:57:40        cri

Kakakin MDD ya sanar a ranar Talata cewa, matsayar MDD game da yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris ta shekarar 2015 ba za ta canzawa ba, duk da matakin da Amurka ta dauka na ficewa daga yarjejeniyar.

Stephane Dujarric, kakakin MDD ya bayyana a taron menema labarai kwana guda bayan MDDr ta karbi sanarwar ficewar Amurkar, ya ce matsayar da MDD ta dauka na aiwatar da yarjejeniyar ta Paris yana nan daran babu sauyi.

Dujarric ya ce, za su ci gaba da karfafa gwiwar mambobin kasashen duniya da su kara azama gabanin babban taron sauyin yanayi na COP25 a birnin Madrid wanda aka shirya da nufin warware matsalolin sauyin yanayi, yana kafa hujja da babban taron bangarorin kasa da kasa kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD wanda za'a gudanar a watan Disamba.

Bisa ga tanadin dokokin yarjejeniyar Paris, kasar Amurka ta sanar da matsayarta ta ficewa daga yarjejeniyar daga ranar 4 ga watan Nuwambar shekarar 2019, ta hanyar bayar da rubutacciyar sanarwa ga babban sakataren MDD.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China