Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yankin Beijing-Tianjin-Hebei na Sin ya samu karuwar fasahar kirkire-kirkre da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba
2019-11-06 10:51:22        cri

Wasu alkaluma da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar na nuna cewa, shirin kasar Sin na raya yankin musamman na Beijing-Tianjin-Hebei ya samar da fasahar kirkire-kirkire da ma ci gaban yankin ba tare da gurbata muhalli ba.

Hukumar ta ce, alkaluman raya yankin, ya kai maki 160.13 a shekarar 2018, karuwar maki 6.14 kan na shekarar da ta gabata. Alkaluman dake wakiltar matsakaicin maki 8.49 na ci gaban da ya samu a shekara daga shekarar 2013 zuwa shekarar 2018, karuwa mafi sauri da yankin ya samu a shekara tsakanin shekarar 2010 da 2013.

Bugu da kari, yankin ya samu karuwar maki 4.71 a fannin kirkire-kirkire da karuwar makin da ya kai 3.61 a fannin ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba daga shekarar 2017. Haka kuma, yankin ya samu karuwar kaso 3.36 cikin 100 na kudaden da ya kashe a fannin bincike da ci gaba zuwa kayayyakin da ake samarwa a cikin gida, na makin da ya kai kaso 0.37 cikin 100, sama da na shekarar 2013.

A bangaren ingancin iska kuwa, matsakaicin ma'aunin ingancin iska na PM 2.5 da ke haddasa hazo, ya yi kasa da kaso 48.1 cikin 100 a cikin shekaru biyar da suka gabata.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China