Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yara sama da 85500 ne ba su zuwa makaranta a yankunan da ake rikici na Kamaru
2019-11-06 10:05:42        cri

Asusun tallafawa kananan yara na MDD (UNICEF) ya bayyana cewa, kimanin yara 855,000 ne ba su zuwa makaranta a yankin arewa maso yammaci da yankin kudu maso yammacin kasar Kamaru, sakamakon tashin hankalin da aka shafe shekaru uku ana yi a wadannan yankuna.

Mai magana da yawun MDD Stephane Dujarric, ya ruwaito wasu alkaluma na asusun na UNICEF na cewa, a cikin watanni biyu na sabuwar shekarar karatu, kimanin kaso 90 cikin 100 na makarantun firamaren gwamnati a wadannan shiyyoyi biyu, gami da kaso 77 cikin 100 na sakandaren gwamnati ne aka rufe ko ba a koyarwa.

Ya ce, muddin bangarorin da rikicin ya shafa ba su dauki matakan da suka wajaba na kare harkar ilimi ba, hakika makomar wadannan yara na cikin hadari.

A halin da ake ciki, asusun na UNICEF, ya bullo da wani shiri na koyarwa na al'umma, inda ake samarwa yaran kayayyakin koyo da amfani da gidajen rediyo don yakar jahilci da ba da darussa don taimakawa yaran, yayin da ba su zuwa makaranta.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China