Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kammala bikin baje koli mafi girma na "Canton Fair" na kasar Sin
2019-11-05 09:50:57        cri

An kammala bikin baje koli mafi girma na kasar Sin da aka fi sani da "Canton Fair" a ranar Litinin din da ta gabata a lardin Guangdong na kasar ta Sin, inda aka samu karuwar masu sayayya da ma fitar da kayayyaki zuwa kasashe da yankunan dake cikin shawarar ziri daya da hanya daya.

Ana dai gudanar da bikin baje kolin shige da ficin kayayyaki na Canton Fair ne sau biyu a shekara, kuma bikin na wannan karo shi ne na 126, an kuma samu ribar sama da dala biliyan 11.06 daga kayayyakin da aka fitar zuwa kasashe da yankunan dake cikin shawarar ziri daya da hanya daya, karuwar kaso 14.81 cikin 100 kan makamancin lokaci na bara, adadin da ya tassama kaso 37.75 cikin 100 na baki dayan cinikin da aka yi.

Alkaluma na nuna cewa, masu sayayya daga kasashe da yankunan dake cikin shawarar ziri daya da hanya daya da suka halarci bikin na bana, ya karu da kaso 1.03 cikin 100 kan makamancin lokaci na bara, adadin da ya kai 85,445.

Mai magana da yawun bikin baje kolin, Xu Bing, ya bayyana cewa, a 'yan shekarun baya-bayan nan, bikin baje kolin na Canton Fair, ya zama muhimmin dandali dake bunkasa harkokin kasuwanci tsakanin kasar Sin da kasashe da yankunan dake cikin shawarar ziri daya da hanya daya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China