Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'ar MDD ta jinjinawa matakin kasancewar bangarori daban-daban a duniya da Sin take dauka
2019-11-04 10:41:01        cri
Darektar zartaswa ta Hukumar Kiyaye Muhalli ta MDD wato UNEP a takaice Inger Anderson ta bayyana a Nairobi, fadar mulkin Kenya cewa, duniya na bukatar manufar kasancewar bangarori daban-daban, kuma Sin tana taka rawa wajen yayata wannan tsari.

Inger Anderson ta shaidawa manema labarai cewa, duniya na bukatar manufar kasancewar bangarori daban-daban, musamman a halin yanzu da muke fuskantar matsalolin da suka shafi yanayi, kusan babu wani yanki da ba ya fuskantar wannan matsala, duk duniya na fama da ita, don haka, ya dace duniya baki daya ta dauki mataki. Ta nanata cewa, kamata ya yi mu kara maida hankali kan batutuwan da suka shafi yanayi. Tana mai cewa, tana farin ciki sosai ganin yadda Sin take taka rawa yadda ya kamata wajen ingiza kasancewar bangarori daban-daban a duniya, kuma kasar Sin muhimmiyar abokiyar huldar kasashen duniya ce ta fuskar tinkarar sauyin yanayi. Ta ce, a 'yan shekarun baya-bayan nan, Sin ta nunawa duniya kyakkyawar hanyar samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China