Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude taron UNIDO a UAE
2019-11-04 09:53:33        cri

An bude taron hukumar raya masana'antu ta MDD (UNIDO) karo na 18, jiya Lahadi a Abu Dhabi, babban birnin hadaddiyar daular Larabawa(UAE).

Taron na wannan karo, zai mayar da hankali ne kan muhimmiyar rawar da ci gaban masana'antu mai dorewa zai taka wajen cimma nasarar ajandar 2030, musamman a bangaren juyin juya halin raya masana'antu na hudu.

A jawabinsa na bude taron, babban darektan hukumar UNIDO, Li Yong ya bayyana cewa, nan da shekarar 2030, hukumar tana fatan ganin masana'antu sun zauna da gindinsu da kyakkyawar makoma, kana za su iya samar da madogara ga kowa da kowa a dukkan kasashen duniya.

Ya kara da cewa, kalubalen da duniyarmu take fuskanta, na bukatar tabbaci da karfin hali. Haka kuma hanyoyin magance wadannan matsaloli, sun dogara kan alaka tsakanin gwamnatoci da ma sassa masu zaman kansu.

Yayin taron na kwanaki biyar, za a baje kolin nasarorin da aka cimma a fannin hadin gwiwar fasaha da alaka, tare da mayar da hankali kan muhimman batutuwan dake shafar kasashe mambobin hukumar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China