Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta kaddamar da gangamin wayar da kan matasa na tsawon wata guda
2019-11-02 15:26:15        cri

Tarayyar Afrika AU, ta kaddamar da gangamin wayar da kan matasa na tsawon wata 1, da nufin samar da damarmaki kai tsaye ga matasan nahiyar miliyan 1.

AU ce ta kirkiro watan na matasan Afrika, inda zai kunshi jerin shirye-shirye a fadin watan Nuwamba, wadanda za su dace da shirin "One Million by 2021" wanda ke da burin samar da damarmaki kai tsaye ga matasa miliyan 1 na nahiyar, a fannonin ilimi da aikin yi da kasuwanci da sana'o'i.

A cewar AU, gangamin na da burin kara wayar da kai a fadin nahiyar, dangane da muhimmancin karfafawa matasa.

Sanarwar da AU din ta fitar jiya, ta ruwaito cewa, an gina gangamin ne bisa tubali mai karfi na kulla dangantaka tsakanin masu ruwa da tsaki domin matasa su amfana. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China