Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tsarin tafiyar da harkokin kasar Sin yana kara kyautatuwa
2019-11-01 19:06:00        cri

Yau gidan rediyon kasar Sin ya gabatar da wani sharhi mai taken "Tsarin tafiyar da harkokin kasar Sin yana kara kyautatuwa", inda aka bayyana cewa, yanzu haka wasu kasashen duniya suna fatan yin koyi da fasahohin da kasar Sin ta samu wajen raya kasa, wannan bayani ya fito ne daga cikakken taro na hudu na kwamiitn kolin JKS na 19 wanda aka kammala jiya a nan birnin Beijing, wato dalilin da ya sa kasar Sin ta samu ci gaba cikin sauri shi ne domin kasar Sin ta bullo da tsarin tafiyar da harkokin kasa mai sigar musamman na kasar Sin, muddin aka nace da kuma kyautata jagorancin JKS, kana aka raya kasa ta hanyar yin amfani da tsarin tattalin arziki iri daban daban, haka kuma aka mai da hankali kan babbar moriyar al'ummun kasar, to, babu shakka za a cimma burin raya kasa cikin lumana.

Yayin taron da aka kammala jiya, an kuma fitar da wani shirin da za a aiwatar da shi bisa matakai uku wato nan da shekarar 2021, cika shekaru 100 da aka kafa JKS, da shekarar 2035, da kuma shekarar 2049, cika shekaru 100 da aka kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin, ban da haka an kuma tabbatar da cewa, za a fara gudanar da muhimman ayyuka 13 a kasar nan ba da dadewa ba.

Sharhin ya jaddada cewa, tarihin ci gaban duniya ya shaida cewa, bai dace ba wata kasa ta tafiyar da harkokinta ta hanyar kwaikwayon tsarin wata kasa, wannan ya sa kasar Sin ta kafa tsarin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin wanda ya fi mai da hankali kan moriyar al'ummunta, ta haka ne kasar Sin za ta kara fito da abubuwa ban al'ajabi yayin da take kokarin raya kasa, da kara samar da damammaki ga sauran kasashen duniya.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China