Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ci gaban nahiyar Afrika zai kai kaso 3.6 a badi
2019-11-01 11:23:27        cri

Wani rahoton nazarin ci gaban nahiyar Afrika na bana da Asusun bada lamuni na duniya ya gabatar jiya a hukumar ECA mai kula da tattalin nahiyar Afrika, a birnin Addis Ababa, ya ce ci gaban nahiyar Afrika zai karu zuwa kaso 3.6 a shekarar 2020 daga kaso 3.2 da ya kasance a bana.

Rahoton na IMF, ya ce hasashen ci gaban ya nuna cewa, ci gaban zai yi tafiyar hawainiya fiye da yadda aka yi hasashe a baya a kimanin 2 bisa 3n kasashen yankin.

Da yake gabatar da rahoton, shugaban sashen raya nahiyar Afrika na asusun, Papa N'diaye, ya ce an yi hasashen ci gaban zai kasance mai karfi a kasashen marasa karfin albarkatu, kan matsacin mataki na kaso 6, yayin da zai yi tafiyar hawainiya a kasashe masu arzikin albarkatu, kan kaso 2.5.

Kuma a kasashe 24 masu kimanin al'umma miliyan 5, kudin shigar da kowanne dan kasa ke samu zai karu cikin sauri fiye da na sauran kasashen duniya, yayin da aka yi hasashen kudin shigar kowanne dan kasa a kasashe 21 zai yi kasa da matsakaicin matakin na duniya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China