Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Akwai bukatar kasashen Afirka su rungumi dabarun zamani domin bunkasa samar da abinci in ji jami'ar AU
2019-11-01 11:10:01        cri

Kwamishiniyar kungiyar AU mai lura da raya tattalin arziki a yankunan karkara da harkokin noma Josefa Sacko, ta yi kira ga kasashen nahiyar da su rungumi dabarun zamani, domin bunkasa samar da abinci da cimaka mai gina jiki.

Jami'ar ta yi wannan kira ne, albarkacin taro na 10, na ranar abinci da cimaka mai gina jiki ta Afirka ko ADFNS a takaice, wadda a bana ke da taken "rungumar fasahohin noma na zamani da inganta cimaka a nahiyar Afirka."

Josefa Sacko ta ce, amfani da fasahohin noma na zamani na iya samar da damammaki, na sauya yanayin da ake ciki na karancin abinci da cimaka mai gina jiki.

Daga nan sai ta bukaci daukacin sassan masu ruwa da tsaki da su yi hadin gwiwar shirya wani baje koli, a daya daga kasashe mambobin AU, wanda zai ba da damar nuna nau'o'in abinci da cimaka da ake da su a nahiyar, su kuma shigar da sassa masu zaman kansu, cikin tsarin shiryawa da kuma gudanar da baje kolin. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China