Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD: Mutane kimanin miliyan 45 na fuskantar matsalar karancin abinci a kudancin Afirka
2019-11-01 10:55:21        cri

Mataimakin kakakin babban magatakardar MDD Farhan Haq, ya ce kimanin al'ummun kasashen kudancin Afirka miliyan 45 ne za su fuskanci matsalar karancin abinci cikin watanni 6 masu zuwa.

Farhan Haq, ya ce hukumar abinci da aikin gona ta MDD, da hukumar shirin samar da abinci na kasa da kasa, tare da Asusun bunkasa aikin gona da ci gaba na kasa da kasa IFAD ne suka yi wannan gargadi.

A cewar jami'in na MDD, akwai sama da mutane miliyan 11 da a yanzu haka ke fuskantar matsalar ko dai karancin abinci, ko ma yanayi na bukatar gaggawa ta abinci a kasashe 9 dake wannan yanki na Afirka.

Kungiyoyin na kasa da kasa dai sun ce 6 daga wadannan kasashe da matsalar ta fi shafa, sun hada da jamhuriyar dimokaradiyyar Congo, da Malawi, da Mozambique, da Tanzania, da Zambia da kuma kasar Zimbabwe.

Wadannan kasashe dai sun samu cikakkiyar damina daya ce tak cikin shekaru 5, kuma fari da iska mai karfi dake lalata amfanin gona, tare da matsalar ambaliyar ruwa sun haifar da gagarumin cikas ga yankin, wanda mafi yawan al'ummar sa ke dogaro da ruwan sama domin noma, kana mafi yawan mutanen sa kananan manoma ne. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China