Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwararru sun bayyana bukatar samar da managartan manufofin ba da kariya ga 'yan ci ranin Afirka
2019-11-01 10:50:57        cri

Wani taro na kwararru daga kasashen Afirka, ya amince da bukatar samar da managartan manufofin da za su taimaka, wajen baiwa 'yan ci ranin Afirka dake ayyukan kwadago a yankunan Gabas ta Tsakiya da yankin Gulf kariyar da ta dace.

Taron wanda ya gudana a jiya Alhamis, a helkwatar kungiyar AU dake birnin Addis Ababan kasar Habasha, ya hallara kwararru da masu shirya manufofi daga kasashen Afirka, dake da yawan masu fita ci rani a kasashen Gabas ta Tsakiya da yankin Gulf ko GCC a takaice.

Mahalartan sun tattauna game da dabarun da ya kamata a bi, don tabbatar da cewa, dandazon 'yan Afirka masu fita ci rani a wadannan yankuna sun samu kariya bisa doka

Da take tsokaci game da batun, daraktar harkokin zamantakewar al'umma a kungiyar AU Mariama Cisse, ta jaddada muhimmancin dake akwai ga kasashen Afirka, da su yi koyi daga manufofin da wasu sassan duniya suke aiwatarwa, game da kare 'yan ci rani, musamman karkashin yarjejeniyar Colombo da shawarwarin birnin Abu Dhabi, wadanda suka taimaka matuka wajen kyautata rayuwar 'yan ci ranin nahiyar Asiya dake ayyuka a kasashen dake yankin Gulf.

Shirin hadin gwiwa domin lura da 'yan ci rani, da bunkasa yankunan Afirka ko JLMP ne ya dauki nauyin shirya wannan taro. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China