Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Fasahar 5G za ta ingiza ci gaban tattalin arzikin kasar Sin
2019-10-31 19:10:38        cri

Yau Alhamis gidan rediyon kasar Sin ya gabatar da wani sharhi mai taken "Fasahar 5G da ake amfani da ita a fannin kasuwanci za ta ingiza ci gaban tattalin arzikin kasar Sin", inda aka bayyana cewa, yau 31 ga watan Oktoba, kasar Sin ta sanar da cewa, za ta fara yin amfani da fasahar 5G a bangaren kasuwanci a hukumance, lamarin da zai kawo babban sauyi ga zaman takewar al'ummar kasar Sin, ba ma kawai tsarin zai ingiza ci gaban tattalin arzikin kasar Sin ba, har ma zai taka rawa wajen ci gaban tattalin arzikin duniya, sanin kowa ne cewa, fasahar 5G za ta kyautata rayuwar Sinawa, haka kuma za ta kyautata yanayin da kasar Sin ke ciki a bangarori daban daban, da ma ciyar da tattalin arzikin kasar Sin gaba yadda ya kamata.

Sharhin ya yi nuni da cewa, 5G fasaha ce wadda za ta amfanawa daukacin bil Adama, har kullum kasar Sin tana son more sabbin fasahohin da ta samu kamar 5G tsakaninta da sauran kasashen duniya, yanzu kasar Sin tana kokarin bullo da sabbin hanyoyin amfanin fasahar 5G ta hanyar daukar hakikanin matakai domin ciyar da tattalin arzikin kasar Sin da kuma na duniya gaba, wannan hakki ne dake bisa wuyan kasar Sin a matsayinta na babbar kasa a duniya a bangaren ci gaba.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China