Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa
2019-10-31 19:07:59        cri

Yau Alhamis gidan rediyon kasar Sin ya gabatar da wani sharhi mai taken "Kasar Sin tana ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa", inda aka bayyana cewa, kwanan baya cibiyar nazari ta ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta fitar da wani rahoto game da ci gaban da kasar Sin ta samu a bangaren bude kofa ga kasashen ketare a shekarar 2019, inda aka nuna cewa, yanzu adadin jarin wajen da aka zuba a kasar Sin da adadin jarin da kasar Sin ta zuba a kasashen waje sun kai matsayi na biyu a fadin duniya, kana kasar Sin ta ci gaba da kasance kasa ta biyu wajen samun jarin waje a cikin watanni shida na farkon bana, lamarin da ya nuna cewa, ba ma kawai kasar Sin tana samun ci gaba a cikin kasar ba, har ma ta samar da karin damammakin ci gaba ga sauran kasashen duniya.

Sharhin ya kara da cewa, manufar bude kofa wata alama ce ta kasar Sin a zamanin da ake ciki yanzu, kasar Sin tana ciyar da tattalin arzikinta gaba cikin sauri ta hanyar taimakawa harkokin cinikayyar waje da kuma kara samun jari daga ketare, ban da haka ci gaban da kasar Sin ta samu ya ingiza karuwar tattalin arzikin duniya, musamman ma tun bayan shekarar 2016, gudummowar da kasar Sin take bai wa karuwar tattalin arzikin duniya ta fi na daukacin sauran kasashen duniya.

Sharhin ya jaddada cewa, sakamakon da kasar Sin ta samu ya nuna cewa, ya dace a kara habaka cudanyar tattalin arzikin duniya, tare kuma da bude kofa ga juna, kasar Sin ita ma za ta ci gaba da kara kokari domin ingiza tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa a nan gaba.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China