Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan Birtaniya ya ce zaben wuri a kasar zai kasance mai tsauri
2019-10-30 14:14:25        cri
Shugabannin siyasa a Birtaniya, sun yi tsokaci bayan majalisar dokokin kasar ta kada kuri'ar gudanar da babban zaben kasar a ranar 12 ga watan Disamba, inda Fira ministan Boris Johnson ya yi hasashen zaben da za a yi cikin makonni 6 masu zuwa, zai kasance mai tsauri.

A jiya da daddare ne mambobin majalisar suka kada kuri'a 438 da suka amince da bukatar gwamnatin Birtaniya ta gudanar da zabe a ranar 12 ga watan Disamba, wanda ya kasance nasara ga Boris Johnson, da majalisar ta yi ta samun nasara a kansa dangane da yunkurinsa na janye kasar daga EU tun bayan da ya kama aiki a watan Yuli.

Shugaban babbar jam' iyyar adawa ta Labour Jeremy Corbyn, ya bayyana zaben a matsayin wata dama ta sauya Birtaniya, wadda ba kasafai ake samunta da kuma raya muradun jama'a.

Shi kuwa Jo Swinson, shugaban jam'iyyar Liberal Democrats mara rinjaye, ya ce babban zaben ne zai yanke shawara game da makomar kasar cikin karni da dama. Ya ce dama ce ta zabar gwamnatin da za ta dakatar da Birtaniya daga ficewa daga EU.

Jam'iyyar Liberal ita ce wadda ke da karfin hana ficewar kasar daga Tarayya Turai. ( Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China