Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan Nijeriya a garuruwa dubu daya sun iya kallon TV dake aiki da tauraron dan Adam
2019-10-30 14:10:12        cri


Jiya Talata, a birnin Abuja, fadar mulkin kasar Nijeriya, aka sanar da kammala shirin "kallon talabijin dake aiki da tauraron dan Adam a wasu garuruwan Nijeriya" da gwamnatin kasar Sin ta taimaka wa kasar Nijeriya wajen gudanarwa. Lamarin da ya nuna cewa, 'yan kasar Nijeriya na garuruwa guda dubu daya sun iya kallon shirye-shiryen talabijin dake aiki da tauraron dan Adam masu inganci, kuma ba tare da kashe kudi sosai ba.

Shirin "kallon talabijin dake aiki da tauraron dan Adam a garuruwa dubu 10 na Afirka" daya ne daga cikin matakan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, wadanda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar yayin taron dandalin tattauna hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka da aka yi a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu a shekarar 2015. Burin wannan shiri shi ne, ba da taimako ga garuruwa guda dubu 10 a kasashen Afirka don su iya kallon talabijin dake aiki da tauraron dan Adam, ta yadda al'ummomin kasar za su kara jin dadin zaman rayuwarsu ta fuskar al'adu da kuma inganta musayar al'adu a tsakanin al'ummomin Sin da Afirka.

Bisa labarin da aka samu, an ce, ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta tsara wannan shiri, kuma kamfanin Startimes ya dauki nauyin gudanar da ayyukan da abin ya shafa. A yayin bikin taya murnar kammala shirin a kasar Nijeriya, mashawarcin jakada kan harkokin kasuwanci na kasar Sin dake kasar Nijeriya Li Yuan ya bayyana cewa, "An riga an gina shirin talabijin dake aiki da tauraron dan Adam a garuruwa dubu daya na Nijeriya, a halin yanzu, al'ummomin kasar, musammam ma wadanda suke karkara mai nisa za su iya kallon shirye-shiryen talabiji masu inganci, kuma yaran Nijeriya da yawa za su koyi ilmi ta hanyar kallon shirin ba da ilmi a talabijin. Muna godiya matuka dangane da goyon bayan gwamnatin kasar Nijeriya, da kokarin da masu fasahohi na kasar Nijeriya suka yi da kuma ayyukan da kamfanin Startimes ya yi don kammala wannan shiri cikin nasara."

Kasar Nijeriya kasa ce mafi yawan mutane a duk fadin nahiyar Afirka, har yawan mutanen kasar ya kai miliyan dari 2, amma na'urorin rediyo da na talabijin na kasar ba su da inganci sosai. A ranar 14 ga watan Janairun bana, aka kaddamar da shirin "kallon talabijin dake aiki da tauraron dan Adam" a kasar Nijeriya, wanda ya kunshi jihohi guda 36 na kasar da kuma babban birnin Abuja. Bisa wannan shiri, an sa na'urar samar da hotunan bidiyo da talabijin a fili, da kuma samar da na'urorin talabiji ga gidaje guda 20 cikin ko wane gari, adadin dake kan gaba a duk fadin kasashen Afirka.

A yayin bikin, shugaban kwamitin labarai na majalisar wakilan kasar Nijeriya Odebunmi Olusegun Dokun ya bayyana cewa, kammala shirin cikin nasara a kasar Nijeriya zai karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu tare kuma da zurfafa mu'amalar dake tsakanin al'ummomin kasashen biyu. Ya kara da cewa, "Shirin kallon talabijin dake aiki da tauraron dan Adama zai tallafawa 'yan kasar Nijeriya da yawa, a madadin wadannan mutane, ina son taya murnar kammaluwar wannan shiri, da kuma godiya matuka dangane da kokarin da kamfanin Startimes ya yi."

A shekarar 2010, kamfanin Startimes ya yi hadin gwiwa da hukumar kula da harkokin talabijin na kasar Nijeriya, wato NTA wajen kafa reshensa a kasar Nijeriya, kuma 95% na ma'aikatan kamfanin mazaunan kasar ne, ya zuwa yanzu, kamfanin yana watsa shirye-shiryensa a birane 66, kana kimanin mutane miliyan 4 suna kallon shirye-shiryen kamfanin, adadin dake kan gaba cikin kasashen Afirka.

Babban jami'in zartaswa na kamfanin Startimes dake Najeriya Zhang Junqi ya yi bayanin cewa, ba kallon talabijin dake aiki da tauraron dan Adama shirin ya samar ga mutanen kasar kadai ba, har ma da koyar da masu fasaha da dama a kasar.

Bisa labarin da aka samu, an ce, sarakuna na jihohin Bauchi, Ekiti, Kano da kuma Lagos da dai sauransu, sun halarci bikin taya murnar kammala shirin, inda suka nuna godiya ga gwmnatin kasar Sin da kamfanin Startimes domin taimakon da suka baiwa kasar. Suna mai cewa, shirin ya sa al'ummomin garuruwansu za su iya kallon shirye-shiryen talabijin mai inganci kuma mai araha, tare kuma da kara sani da fahimtar su game da kasar Sin, har ma da kasashen duniya baki daya. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China