Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manzon MDD: Dogaro kan kwamitin tsarkake mulki kawai ba zai iya daidaita rikicin Syria ba
2019-10-29 11:59:18        cri

 


Yayin da ake shirin bude taron farko na kwamitin tsarkake mulkin kasar Syria, Geir Pederson, manzon musamman mai kula da batun Syria na MDD, ya kira wani taron manema labaru a Geneva na kasar Switzerland a jiya Litinin, inda ya ce yadda za a kaddamar da kwamitin tsarkake mulkin ya ba da damar kawo karshen yakin basasa a Syria, wanda ya dade har shekaru 8 yanzu. Sai dai a sa'i daya ya nanata cewa, ba za a samu damar daidiata rikici a kasar ba, idan aka dogaro kan wannan kwamiti kadai.

A wajen taron manema labarun da aka yi jiya, Geir Pederson ya ce, mambobi 150 na kwamitin tsarkake mulkin kasar Syria, suna kan hanyar zuwa Geneva, inda za su fara aiki karkashin taimakon MDD. Sa'an nan za a kaddamar da kwamitin a hukumance a gobe Laraba.

A ganin Pederson, kafuwar kwamitin ya nuna nasarar da gwamntin kasar Syria da masu adawa da ita suka cimma, bisa kulla wata yarjejeniyar siyasa a karon farko, lamarin da ya samu amincewa daga gamayyar kasa da kasa. Pederson ya ce,

"A ganina, wannan wata nasara ce da aka samu tun bayan da kwamitin sulhu na MDD ya zartas da kuduri mai lamba 2254 a watan Disamban shekarar 2015, inda a karon farko bangarori daban daban na duniya suka cimma ra'ayi daya wajen daukar wani muhimmin mataki don daidaita rikicin Syria. Bangarorin da suka hada da kasashen Rasha, Turkiya, da Iran, gami da wasu kasashen yammacin duniya da na Larabawa. Sa'an nan, mambobin kwamitin sulhun MDD su ma sun cimma matsaya wajen amincewa da matakin."

Bisa yarjejeniyar da gwamnatin Syria da bangaren masu adawa da ita suka kulla, kwamitin tsarkake mulki zai iya gyara kundin tsarin mulki na yanzu, ko kuma sake tsara wani sabo. Cikin mambobin 150 na kwamitin, akwai wasu 50 da gwamnatin Syria ta gabatar da sunayensu, da wasu 50 da suka zo daga bangaren masu adawa da gwamnatin, gami da wasu 50 dake wakiltar fararen hula. Sa'an nan daga cikin kowane bangarensu za a zabi wasu 15 domin su kafa wata tawagar tsara tsarin mulki.

A fannin tsarin da ake bi wajen tabbatar da wata manufa, kwamitn tsarkake mulkin zai dauki dabarar tattaunawa don cimma ra'ayi daya. Idan an kasa cimma matsaya, sai a bi hanyar jefa kuri'a. Ko a cikin tawagar tsara tsarin mulki ne, ko kuma a cikin kwamitin gaba daya, idan ana son zartas da wani kuduri, to, dole ne a samu kuri'un amincewa da yawansu ya kai kashi 75% ko kuma fiye da haka.

Wasu na ganin cewa, matsayin kashi 75% da aka sanya ya yi yawa sosai, watakila zai haifar da tsaiko ga aikin tsara tsarin mulki. Amma a ganin Geir Pederson, duk tsawon lokacin da za a kwashe, kwamitin tsarkake mulkin zai ci gaba da aikinsa. Ya ce,

"Gwamnatin kasar Syria da masu adawa da ita sun riga sun yarda da gudanar da aikin tsara tsarin mulki cikin sauri, ba tare da jinkiri ba. Ko da yake ba mu san tsawon lokaci da za su bukata ba, amma matukar sun yi aiki tukuru, to, za mu ga ci gaba, wanda zan gaya ma kwamitin sulhun nan take. Na yi Imani za a samu wani sakamako mai kyau."

Pederson ya ce yana sa ran ganin kafuwar kwamitin tsakake mulkin ta samar da damar rage radadin da jama'ar kasar Syria suke ji a zaman rayuwarsu. Sai dai bai kamata a yi biris da wasu matsalolin da ake fuskanta yanzu ba, wadanda suka hada da barkewar rikici a kai a kai a wurare daban daban na kasar Syria, da dubun-dubatar mutanen Syria da aka garkame su, da sace su, da wadanda suka yi batan dabo, da dai makamantansu. Mista Pederson ya ce bai sanya wani babban buri ba yanzu, kawai yana fatan kwamitin zai samar da damar daukar karin matankan siyasa a kasar. Ya ce,

"Mun fahimci yanayin da muke ciki sosai, wato bisa dogaro kan wannan kwamitin kadai, sam ba za a samu damar daidaita rikicin Syria ba."

Sa'an nan yayin da yake amsa tambayoyin da aka yi, mista Pederson ya ce, akwai Kurdawa a cikin mambobin kwamitin tsarkake mulkin, amma ba su wakiltar sojojin Kurdawa na SDF. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China