Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Burtaniya ta sake tsawaita aikin ficewar kasa daga EU
2019-10-29 10:54:40        cri

Shugaban kwamitin kungiyar tarayyar kasashen Turai ta EU Donald Tusk‎ ya bayyana a jiya Litinin cewa, mambobin kungiyar EU guda 27 sun yarda da rokon kasar Burtaniya game da tsawaita aikin ficewar kasar daga kungiyar EU zuwa ranar 31 ga watan Janairun shekarar 2020.

Majalisar wakilai ta kasar Burtaniya ta zartas da wani daftari a ranar 19 ga wata, inda ta tsawaita lokacin kada kuri'u kan sabuwar yarjejeniyar ficewar kasar Burtaniya daga kungiyar EU, wadda firaministan kasar Boris Johnson ya kulla da kungiyar EU, kuma ta bukaci Boris Johnson da ya mika sakon ga kungiyar EU domin sake tsawaita aikin ficewar kasa daga kungiyar EU.

A wannan rana kuma, firaminista Johnson ya gabatar da sakon ga Donald Tusk, domin neman iznin tsawaita ranar ficewar kasar Burtaniya daga kungiyar EU daga ranar 31 ga watan Oktoban bana, zuwa ranar 31 ga watan Janairun shekarar 2020. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China