Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'an tsaron Somali da AU za su yi hadin gwiwa don dakile amfani da ababen fashewa a kasar
2019-10-29 10:30:17        cri
Masu ruwa da tsaki a harkokin tsaron kasar Somali sun sha alwashin kawo karshen yin amfani da abubuwan fashewa IEDs wadanda mayakan al-Shabab ke amfani dasu wajen kaddamar da hare hare kan al'umma a kasar ta gabashin Afrika.

A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da aka fitar ranar Litinin bayan wani taron karawa juna sani na kwanaki biyu da aka gudanar a Mogadishu, masu ruwa da tsaki sun lura cewa, IEDs har yanzu sun kasance daya daga cikin abubuwan da 'yan ta'adda ke amfani dasu a matsayin makaman da suke kai hare hare kan tawagar jami'an kiyaye zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika a Somalia wato (AMISOM), da jami'an tsaron kasar Somaliya, da kuma fararen hula dake tafiye tafiye a sassan kasar.

Mahalarta taron na hadin gwiwa tsakanin AMISOM, da hukumar bada taimako ta MDD UNMAS, da dakarun sojin Birtaniya wato British Army suke shirya, sun ce hare haren, sun yi sanadiyyar dakatar da zirga zirgar mutane da kayayyaki, da kuma jigilar kayayakin ayyukan jin kan bil adama.

Simon Mulongo, wakilin musamman na hukumar gudanarwar AU a Somalia, ya ce abubuwan fashewar IEDs suna daga cikin manyan ginshikan da AMISOM ke yaki dasu a aikin yaki da ta'addanci.

Mahalarta taron karawa juna sanin sun tattauna batutwa dake shafar matakan turawa da kuma horas da dakarun AMISOM da takwarorinsu dakarun tsaron kasar Somali, da yadda za'a kawar da yaduwar abubuwan fashewa a Somalia, da kuma dakile amfani da abubuwan fashewar a kasar baki daya.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China