Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Trump ya ce an kashe shugaban IS a harin sojojin Amurka a Syria
2019-10-28 10:15:22        cri

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar a jiya Lahadi cewa an hallaka jagoran kungiyar masu fafutukar kafa daular musulunci (IS) Abu Bakr al-Baghdadi a wani harin da sojojin Amurka suka kaddamar a Syria.

Da yake jawabi a fadar White House, Trump ya e, wata rundunar musamman ta sojojin Amurka ta kaddamar da harin ne a daren ranar Asabar da nufin gano al-Baghdadi a arewa maso yammacin Syria, a lokacin ne al-Baghdadi ya kashe kansa ta hanyar sanya wata riga mai bam a jikinta.

A cewar mista Trump babu ko a sojan Amurka guda da ya rasa ransa a lokacin samamen.

Al-Baghdadi, dan shekaru 48, sunansa na asali shi e Ibrahim Awad al-Badri, ya sanar da kafa wata daular musulunci, wacce aka fi sani da IS a watan Yunin 2014.

A shekarar 2016, ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar da biyan tukuicin dala miliyan 25 ga duk wanda ya bayar da bayanan da za su taimaka a kamo ko kuma a kashe jagoran na IS.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba
Ga wasu
v An harbe dakarun kungiyar IS 8 har lahira 2019-09-09 10:56:17

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China