Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi kira ga sa kaimi ga raya ra'ayin bangarori daban daban
2019-10-27 16:41:12        cri
An rufe taron koli na kungiyar kasashe 'yan ba-ruwanmu karo na 18 na kwanaki 2 a birnin Baku dake kasar Azerbaijan a jiya, inda aka zartas da sanarwar Baku ta bada jagoranci ga makomar kungiyar, kana an jaddada cewa, za a kara inganta karfin kungiyar, da sa kaimi ga raya ra'ayin bangarori daban daban da kuma samun zaman lafiya da bunkasuwa a yankin.

A matsayin muhimmin nasara da aka samu a gun taron kolin a wannan karo, sanarwar Baku ta bayyana cewa, kasashe membobin kungiyar za su ci gaba da bin ka'idojin kungiyar, da yin kokarin da ya dace da sabon yanayin siyasa na duniya, da kara karfin kungiyar. Kasashe membobin kungiyar sun yi imani da yin hadin kai don tabbatar da moriyar kasashe masu tasowa tare, da yin kokarin kafa tsarin tafiyar da duniya mai cike da adalci, da fahimtar juna, da amfani a fili.

Sanarwar ta jaddada cewa, kasashe membobin kungiyar sun nuna goyon baya ga tsarin bangarori daban daban dake karkarshin jagorancin MDD, da girmama ka'idojin tabbatar da cikakkun yankuna da ikon mallakar kasa da kasa, da samun 'yancin kai a fannin siyasa, da daina tsoma baki kan harkokin cikin gida na sauran kasashe da sauransu. Kana sanarwar ta ce, kasashe membobin kungiyar za su kara yin kokari wajen yaki da ta'addanci ta hanyoyi daban daban. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China