Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan wasan Afirka da suka halarci gasar wasannin sojoji
2019-10-26 20:22:19        cri

Ana ci gaba da gudanar da gasar wasannin sojoji ta kasa da kasa karo na 7 a birnin Wuhan na lardin Hubei da ke yankin tsakiyar kasar Sin, a yau kuma an fara gasar wasan Taekwondo na matsayin 87 kg tsakanin maza wato nauyin dukkan 'yan wasan da suka shiga gasar bai kai kilogiram 87 ba. Dan wasan kasar Nijeriya Ahmed Shehu Bello bai ci nasara cikin gasar da ya yi da Suaza Gil David Antonio na kasar Colombia ba, bai kasance cikin 'yan wasa 8 mafiya karfi cikin gasar ba. Bayan gasar, wakiliyarmu Tasallah Yuan ta tambaye shi ra'ayinsa kan gasar da ya yi a yau, shirinsa a nan gaba da ayyukan da kasar Sin ta yi wajen shirya gasar.


 

Baya ga Ahmed Shehu Bello kuma, dan wasan kasar Nijer Oumarou Ibrahim shi ma bai taki sa'a cikin gasar da ya yi da takwaransa na kasar Iran Abbasi Mardekheh Babak ba. Shi ma bai kasance cikin 'yan wasa 8 mafiya karfi ba. Bayan gasar, wakiliyarmu Tasallah Yuan ta tambayeshi ra'ayinsa kan gasar da ya yi a yau, ayyukan shiryawa da shirinsa a nan gaba. Ga abun da ya fada.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China