Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kungiyoyin SADC da AU sun yabawa zaben kasar Botswana
2019-10-26 17:07:41        cri
Tawagogin kungiyoyin raya yankin kudancin Afrika wato SADC da ta Tarayyar Afrika AU, masu sa ido kan babban zaben Botswana na 2019, sun yaba da yadda zaben ya gudana, inda suka bayyana shi a matsayin sahihi, wanda kuma ya bayyana muradun al'ummar kasar.

Tawagogin kungiyoyin biyu, sun bayyana haka ne lokacin da suke zantawa da manema labarai da sauran masu ruwa da tsaki, lokacin da ake bayyana kwarya-kwaryar bayanan masu sa ido kan zaben daga kasa da kasa a birnin Gabrone, a jiya Juma'a.

Da yake jawabi ga taron, Sibusiso Moyo, Ministan harkokin wajen Zimbabwe da kula da cinikayyar kasar da kasa da kasa, wanda kuma shi ne shugaban tawagar SADC, ya yabawa yadda aka gudanar da zaben saboda yadda aka tsare gaskiya

A nata bangaren, shugabar tawagar AU kuma tsohuwar mataimakiyar shugaban Gambia, Jallow Fatomata, ta ce sun lura cewa an gudanar da sahihin zabe bisa tabbatar da adalci.

A ranar 23 ga watan Oktoba ne aka gudanar da babban zabe a kasar, inda jam'iyya mai mulkin kasar wato the Botswana Democratic Party, ta lashe zabukan bisa samun kujeru 38 daga cikin 57 na majalisar dokokin kasar, lamarin da ya sa Shugaban Jam'iyyar zama shugaban kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China