2019-10-25 20:38:14 cri |
Wakiliyar kasar Uganda a hukumar ta ATAF Stella Nyapendi ce ta bayyana hakan, yayin zantawa da manema labarai a jiya Alhamis. Tana mai cewa, an kafa hukumar ATAF mai mabobin kasashe 38 ne, yayin da ake fargabar rikicin kudade na duniya na shekarar 2008, ka iya shafar tallafin kudaden da kasashen da suka ci gaba ke baiwa kasashen nahiyar.
Ana ganin hukumar a matsayin kungiya mafi girma a nahiyar, dake kula da batutuwan kudade haraji a duniya dake shafar nahiyar.(Ibrahim)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China