Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta bayyana damuwa dangane da rashin samun ci gaba kan yankin Abyei
2019-10-25 10:45:06        cri

Mataimakin sakatare janar na MDD kan ayyukan wanzar da zaman lafiya, Jean Pierre Lacroix, ya bayyana damuwa kan rashin samun wani ci gaba dangane da matsayin Abyei, yankin da kasashen Sudan da Sudan ta Kudu ke takaddama a kai, duk da cewa an samu ingantuwar dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Jean_Pierre Lacroix ya shaidawa kwamitin sulhu na MDD cewa, ci gaban da aka samu tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu, bai kai kan batun warware matsayin yankin Abyei ba.

Ya ce babu wata tattaunawa da kwamitin hadin gwiwa kan nazarin matsayin yankin ya yi tun daga watan Nuwamban shekarar 2017. Kuma babu wani ci gaba da aka samu dangane da kafa shugabancin hadin gwiwa, ciki har da na hukumar 'yan sanda da kotu da gyare-gyare.

Jami'in ya kara da cewa, yayin da gwamnatin Sudan ta nuna a shirye take ta shiga shirin hadin gwiwa na kafa rundunar 'yan sandan Abyei, Sudan ta Kudu ba ta bayyana nata ra'ayin game da wannan yunkuri ba.

Ya ce wannan abun damuwa ne tun da daukacin yanayin tsaron yankin Abyei na da rauni, la'akari da rikici tsakanin al'ummomi dake ci gaba da aukuwa da karuwar laifuffuka da kuma kasancewar kungiyoyi masu dauke da makamai a yankin lokaci zuwa lokaci. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China