Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na maraba da ganin sake daga matsayin kasar ta fannin kyawun yanayin kasuwanci da bankin duniya ya yi
2019-10-24 20:19:40        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Sin Madam Hua Chunying ta bayyana a yau Alhamis cewa, kasarta na maraba da yadda bankin duniya ya sake daga matsayin kasar ta fuskar kyawun yanayin kasuwanci a duk fadin duniya a cikin rahotonsa kan yanayin kasuwanci na duniya na shekara ta 2020.

Bisa rahoton da bankin duniya ya bayar, matsayin kasar Sin a fannin kyawun yanayin kasuwanci a duniya ya tashi daga na 46 a bara zuwa na 31 a bana, matsayin da ya sanya ta zama cikin kasashe goma wadanda yanayin kasuwancinsu ya kyautatu matuka a cikin shekaru biyu a jere. Madam Hua ta ce, hakan ya nuna cewa, kasar Sin na nuna hazaka wajen zurfafa yin gyare-gyare a gida da kara bude kofarta ga kasashen waje tare kuma da ci gaba da kyautata yanayin kasuwanci da zuba jari, kuma kwalliya ta biya kudin sabulu, al'amarin da ya samu amincewa sosai daga kasashen duniya.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China