Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bankin duniya ya daga matsayin kasar Sin ta fannin kyawun yanayin kasuwanci a duniya
2019-10-24 20:15:38        cri

Bankin duniya ya fitar da wani rahoto kan yanayin kasuwanci na shekara ta 2020 a yau Alhamis, inda matsayin kasar Sin a fannin kyawun yanayin kasuwanci a duniya ya tashi daga na 46 a bara zuwa na 31 a bana, matsayin da ya sanya ta zama cikin kasashe goma wadanda yanayin kasuwancinsu ya kyautatu matuka a cikin shekaru biyu a jere. Kwalliya ta biya kudin sabulu ga kasar Sin wajen zurfafa yin gyare-gyare a gida da fadada bude kofa ga kasashen waje.

Yanayin gudanar da harkokin kasuwanci a kasar Sin na kara kyautata yadda ya kamata bisa doka da oda, abun da ya taimaka ga yin takara cikin adalci. Haka kuma kasar Sin na kara daukar wasu matakai don karfafa gwiwar kamfanonin kasashen waje su zuba jari a kasar. Alal misali, idan kamfani yana son samun izinin amfani da wutar lantarki, akwai bukatar ya bi matakai biyu kuma cikin kwanaki 32 kawai, amma idan yana son samun irin wannan izinin a yankin gabashin Asiya, zai bi matakai fiye da hudu kuma cikin kwanaki 63. A halin yanzu kasar Sin ta zama kasar dake kan gaba wajen jawo hankalin masu zuba jari a duk fadin duniya.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China