Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Aikin jigilar kaya a kasar Sin na taimakawa raya aikin noma
2019-10-24 13:44:35        cri
Hukumar gidan waya ta kasar Sin tana kokarin samar da hidimomi masu inganci ga wurare masu fama da talauci, don taimakawa yunkurin rage talauci a wadannan wurare. Bisa alkaluman da hukumar ta gabatar a jiya Laraba, gidan waya da kamfanonin jigilar kaya sun taimaki wasu gundumomi masu fama da talauci na kasar Sin wajen sayar da amfanin gona ta yanar gizo wato Internet wanda darajarsu ta kai fiye da kudin Sin Yuan biliyan 110, a farkon watanni 6 na bana, inda jimillar adadin ta karu da kashi 29.5% bisa makamancin lokacin bara.

Zuwa yanzu, kamfanonin jigilar kaya na kasar Sin sun riga sun kulla huldar hadin gwiwa tare da wasu wurare 905 na kasar, wadanda kowanensu na sayar da wani kaya ko kuma wani amfanin gonansu ta hanyar Internet. Sa'an nan cikin wadannan nau'ikan kayayyaki, akwai wasu 23 da a kan sayar da wani kaya daga cikinsu har fiye da guda miliyan 10 a kowace shekara. Yayin da a nasu bangare, kamfanoni masu alaka da gidan waya sun kulla yarjeniyoyin tallace-tallacen amfanin gona 1143 a wurare daban daban na kasar Sin, tun daga watan Janairu zuwa Satumban bana, inda aka yi jigilar kayayyakin da aka samar da su a kauyuka da nauyinsu ya kai ton dubu 284 cikin birane domin a sayar da su a can, adadin da ya karu da kashi 69% idan an kwatanta da na makamancin lokacin bara. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China